
Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya ahbarat cewa ya nakalto dagashafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada al’adu na kasar cewa, cibiyar Al yasina kasar Ghana ta dauki nauyin karanta wasikar jagora a wani gidan talabijin na kasar kai tsaye.
Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin shirin sheikh Idris Toyo shugaban cibiyar Al yasin ya bayyana cewa, wasikar ta jagora ta kunshi muhimman lamurra da suke da amfani ga msuulmin duniya baki daya.
Ya kara da cewa bias la’kari da cewa barazanar da ake fuskanta akasashen turai ta shafi sauran yankunan duniya a halin yanzu ta ta’addanci da sunan addini, yana da muhimmanci al’ummomin duniya baki daya su gane cewa addinin msulunci ba addinin ta’addani ba ne, addini ne na zaman lafiya da fahim juna kamar yadda wasika ta nuna.
Daga karshe yay i kira ga dukaknin samari da ma sauran al’ummar musulmi na kasar Ghana da su dauki dukkanin darussan da wannan wasika take koyarwa, tare da isa da wanann sako ga sauran al’ummomin wadanda ba musulmiba.