IQNA

Za A Gyara Dakin Karatu Na Musulunci Mafi Jimawa AKasar Morocco

15:53 - March 15, 2016
Lambar Labari: 3480233
Za A Gyara Dakin Karatu Na Musulunci Mafi Jimawa AKasar Morocco
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gyaran dakin karatu mafi jimawa a kasar Moroccoa garin Fas tun cikin karni na 12 miladiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, ana gudanar da wannan aiki ne a garin na Fas da ke cikin gundumar Qarwin, domin sake gina wannan babban dakin karatu na musulunci.

Ministan mai kula harkokin al’adu na kasar y ace an aksh emiliyoyin daloli a tsawon lokuta wajen sake gina wannan wuri da yi masa gyara da kwaskwarima, wanda aka gyara shi ya zuwa yanzu har sau casein da biyar a tarihi.

An gina wannan katafaren dakin karatu ne tuna cikin shekara ta 859, wanda Fatima Fahri ta gina, wata diyar wani babban attajiri dan kasar Tunisia wanda ya zu ya zauna kasar ta Morocco a yankin Qarwin tsawon shekaru.

Bisa ga bayanan da aka bayar, wasu daga cikin manyan malaman addinin mslunci da suka hada da masana irfani irin su Ibarabi da kuma Ibn Khaldun da wasu masanan na daban duk sun yi karau a wannan wuri a cikin karni na goma sha hudu.

3483295

captcha