
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alyaum 24 cewa, Muhammad Salim Wuld Buk shugaban cibiyar da ke shirya taron gidajen talabijin da radiyo na kasashen musulmi ya bayyana cewa an fara gudanar da wannan babban taro na uku.
Ya ce babban abin da taron zai mayar da hankali a kansa shi ne yadda za a samu matsaya guda wajen fuskantar tunanin kafirta musulmi da kuma ta’addanci da ake yi da sunan addini, wanda hakan ke bata sunan musluncia duniya.
Muhamamd salim ya ce suna yin Allawadai da duk wani aiki na ta’addanci da wasu suke aikatawa da sunan addini ko ba da sunan addini ba a duniya.
Kamar yadda ya yi ishara da irin abin da yan ta’adda na Daesh suke aikatawa, na kona mutane da wuta da ransa, ko kuma saka a cikin keji su nutsar da su a cikin ruwa har sai sun mutu, ko kuma saka musu nakiya da dai sauran hanyoyi na dabbaci da suke, y ace a ina suka samo haka? ba dai cikin addinin muslunci ba.
Shugaban wannan cibiya y ace aiki ne da ya rataya kan dukkanin musulmi da su mike tsaye domin yakar wannan balai da ya kunno kai cikin al’ummar musulmi, ta hanyar wayar da kan musulmin musamman ma matasa wadanda sune aka fi saurin yaudara tare da saka musu irin wannan mmmnan tunani.
Ya ce kafofin yada labaran musulmi suna gagarumar rawar da za su taka wajen ganin an samu tabbatar da wanann manufa, domin kuwa suna hanyoyi na isar da sakon da suke so cikin sauri, kuma ya yi tasiri kamar yadda ake bukata.