IQNA

An Buga Tare Da Watsa Littafin Rayuwar Jagora a Cikin Harshen Ispaniyanci

23:34 - March 17, 2016
Lambar Labari: 3480238
Bangaren kasa da kasa, an buga tare da watsa littafin jagoran juyin islama da aka tarjama cikin harshen Ispaniyanci a madaba’antar Mandala a birnin madrid.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yadda al’adun muslunci na Iran cewa, an tarjama tare da buga littafin rayuwar jagora daga karatun dalibta har zuwa matsayin jagora a cikin harshen Ispaniyanci, wanda Ali Akbar Wilayati ya rubta.

Littafin mai suna "Daga dalibta zuwa Jagora” wanda Ali Akbar Wilayati ya rubuta a cikin shafuka 155, kuma Ali Reza Islama’ili karamin jakadan Iran a Spain ya yi gabatarwa a cikinsa.

Madaba’antar Mandala na daya daga cikin manyan madaba’antu wadanda gwamnatin Spain ta aince da su a kasar, wanda kma shi ne ya buga wannan littafi.

3483994

captcha