
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewa, Abu Talib Mahmud ya rubuta littafi mai suna Sautin masar na makaranta a kasar.
A cikin wannan littafi an rubuta tarihin wasu daga cikin fitattun makaranta kur’ani mai tsarki yan kasar Masar da ska yi suna a duniya ta fuskar karatu.
Koyon karatun kur’ani mai tsarki bisa salon malaman karatun kur’ani na kasar Masar, yana daya daga cikin muhimman lamurra ta fsuakar ci gaba da aka samua duniyar musulmi ta fuskar karatu kur’ani mai tsarki a duniyar yau.
Wannan littafi yana da fasali arbain, kowane daga ciki ya yi Magana a kan daya daga cikin fitattun makaranta kur’ani na kasar Masar, tarihin rayuwarsa da kuma lamurra da suka shafi karatinsa da salinsa da kuma abubwan da ya bari.