IQNA

An Gudanar da Taron Karawa Juna Sani Kan Kur’ani A kasar Senegal

23:46 - March 18, 2016
Lambar Labari: 3480241
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taron karawa juna sani kan kur’ani mai tsarki a birnin Dakar na kasar Senegal da ke yammacin nahiyar Afirka.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta daga Dakar cewa, a jiya nw aka kawo karshen wani taron karawa juna sani kan kur’ani mai tsarki a birnin Dakar na kasar Senegal da ke yammacin nahiyar Afirka tare da halartar masana daga sasas na nahiyar kuma jamhuriyar muslunci.

Dr. Karimi malami a ami’ar Imam Sadeq (AS) ya gabatar da wata makal;a a wurin taron, wadda ta kunshi cewa, shi kur’ani mai tsarki a kowane lokaci yana koyar da dana dam salon rayuwa da ya fi dacewa da shi, kuma nisanta shi daga wuce gona da iri.

Sheikh Sharif Aumbalo shugaban cibiyar Al Yasin ya bayyana cewa, masarautar Saudiyya ce take daukar nayin ayyukan kungiyoyin ta’addanci da sunan jihadi, wanda hakan ke bata sunan muslunci a duniya.

Sayyid hassan Esmati shi ne karamin jakadan Iran a kasar Senegal, wanda kuma shi ne ya shirya wannan babban taro na kasa da kasa, da nufin kara kusanto da fahimtar malamai kan mahangar kr’ani mai tsarki da kuma abubwan da yake koyar da mu, domin mu kasance kan sahihiyar koyarwa ta wannan littafi mai tsarki, maimakon bin ra’ayoyin da suke batar da musulmi da sunan bin kur’ani da sunna.

Abin tuni a nan dais hi ne, wannan shi ne karon farko da aka gudanar da irin wannan taro a kasar ta Senegal, inda aka samu halartar malamai daga bangaroro daban-daban da suka tofa albarkacin bakinsu, kan hadarin da al’ummar musulmi suke fuskanta ta hanayar karkatar da su da wasu ke kokarin yi da sunan suna yada ilimin kur’ani da sunnar manzo, alhali kuwa suna koyar da akidar kafirta musulmi da ta’addanci ne, daga cikin malami da sukahalarta akwai na darikun Sufaye da ska hada da Tijjaniyyah, Muridiyya da kuma mabiya Ahlul bait (S), kamar yadda malamai daga jami’ar Almustafa (SAW) suka halarta.

3484073

captcha