IQNA

An kaddamar Da Wata Sabuwar Cibiyar Kur’ani A Basara

23:57 - March 18, 2016
Lambar Labari: 3480243
Bangaren kasa da kasa, an kaddamar da wata sabuwar cibiyar kur’ani mai tsarkia garin Basara na kasar Iraki mai suna Almostafa (SAW)

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Qaf cewa, a lokacin kaddanar da wannan cibiyar kur’ani ta Almostafa (SAW) sheikh Adnan Salehi shugaban cibiyar kula da ayyukan kur’ani ta Basara, Sheikh Majid Bahrani shugaban Hauzar sadoqain da wasu malami na daban duk sun halarci taron.

Bayanin yaci gaba da cewa an gabatr da karatun kur’ani daga wasu makaranta da suka hada da Hatam Shamhani, Mu’utaz Al-kar, Balal Al-lami, Sayyid Hussain Hussaini, Aziz Muslim da saureansu.

Kamar yadda kuma malai suka gabatar da jawabai a wurin taron domin fadakarwa kan matsayin kur’ani mai tsarki, da kuma yadda ya kamata musulmi su mayar da hankali wajen yin aiki da koyarwarsa a cikin dukaknin lamurra da ska shafi rayuwarsu ta yau da kullum.

3484097

captcha