IQNA

Za A Gudanar Da Taron Maulidin Sayyida Fatima Zahra (SA) A Ingla

23:55 - March 21, 2016
Lambar Labari: 3480251
Bangaren kasa da kasa, cibiyar muslunci ta birnin landan na kasar Birtaniya za ta shirya gudanar da wani zaman taro na maulidin Sayyida Zahra (SA)

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta daga birnin landan na kasar Birtaniy cewa, cibiyar muslunci na shirin gudanar da babban taro na haihuwar Fatima Zahra (SA) tare da halartar masoyanta.

Bayanin ya kara da cewa baya ga wanann taro mai albarka akwai wani babban taron kuma wanda shi ma cibiyar za ta shirya kan tunawa da lokacin haihuwar Amirul muminin Ali (AS).

Wannan cibiya ta isar da wannan sako ga dukaknin masoya iylan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da su halrci taro ana gayyatarsu, musamamn ma mazauna birnin.

3484301

captcha