
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Jollof News cewa, tun bayan da shugaban ksar Gambia ya canja sunan kasar zuwa jamhuriyar muslunci, wasu daga cikin kafofin yada labarai musamman na turai suke ci gaba da bata sunan kasar.
Sharif Bujang ministan yada labaran kasar Gambia ya bayyana cewa, kafofin yada labaran da ke yin hakan suna kokarin tsiorata sauran al’ummomi ne dangane da kasarsa.
Ya ce lokacin da Yahya Jamey a sanar da kasar a matsayin jamhuriyar muslunci ya bayyana cewa, ba zai danne hakkiin kowa ba, ta fuskar saka tufafi da sauransu, domin kuwa yana son ya kawo misali ne dangane da yadda muslunci yake girmama yancin dana dam.
Bujang ya ce a lokacin da shugaban kasar ya bayar da wannan sanarwa ya tabbatar da cewa kasarsa ba zata canja alakarta da kowace kasa ba, kuma har yanzu ba ta canja ba.
Ya kara d cewa shugaban kasarsu yana son ya fito da matsayin addinin muslunci ne sabanin yadda ake ake zato, domin bayyana kyayyawar fuskar muslunci ga sauran al’ummomin duniya.