
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Pahome Page cewa, daliban jami’ar sun wasu shirye-shirye na musamma domin wannan mako.
Bintu fal ita ce shugabar kwamitin daliban musumi na wannan jami’a ta bayyana cewa, sun shirya taron ne da nufin karb kiran da aka yi musu na shirya wannan taro daga dalibai wadanda ba musulmi da suke jami’ar.
Ta ce sun karba kiran ne domin ganin sun yi amfani da wannan damar wajen tabbatar da cewa sun yi bayani ga dalibai wadanda ba muslmi kan muslunci maimakon abin da ake gaya musu kan muslunci wand aba gaskiya ba ne.
Zahra Khawajah tana daya daga cikin dalibai na wannan jami’a, wadda kuma take a matsayin mamba a kwamitin dalibai musulmi na jami’ar wadsanda suka dauki nayin shirya wannan taro na makon sanin muslunci.
Ita ma a nata bangaren ta ce wannan babbar dama ce ta bayyana hakikanin abin da musulunci yake koyarwa, na zaman lafiya da fahimtar juna atsakaninsa dasauran addinai, maimakon abin da ake yadawa na karairayi dangane da shi a ko’ina.