IQNA

Gasar Kur’ani mai Tsarki A Kasar Singapoor

23:33 - March 26, 2016
Lambar Labari: 3480264
Bangaren kasa da kasa, za a fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a kasar Singapoor.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «muis.gov.sg» cewa, masallacin darul Aaman da ke birnin Singapoor a kasar zai dauki nauyin gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki.

Bayanin ya ce shekaru 7 zuwa 12 a bangaren karatu da hardar kur’ani a bangare na farko, sai kuma shekaru 13 zuwa 18 a bangare na biyu, sai kuma 19 zuwa 25 a bangare na uku, wadnda za su fafata da juna a kwanakin da za a share ana gabatar da gasar.

Bangarorin gasar dai sun hada da mata da kumamaza, wanda kuma hakan zai bayar da dama ga kowane bangare ya bayar da gudunmawa wajen yada koyarwar kur’ani mai tsarki.

Babbar manufar shirya wannan gasa dai ita ce, kara yada koyarwar kur’ani a tsakanin mabiya addinin muslunci a kasar ta Singapoor, ta yadda za su kasance masu masaniya a kansa musamman ma dai matasa.

Kasar Singapoor dai tana da fadin kilo mita murabbai 700 a gabashin nahiyar Asia, kuma babban birnin kasar shi ne Singapoor.

Yawan musulmin kasar ya kai kasha 15 cikin dari.

3484544

captcha