
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na 12news.com cewa, da dama daga cikin mutanen da ba musulmi ba sun halarci wannan shiri domin samun masaniya kan wannan addini.
Shahir Shafi daya daga cikin wadanda suka shirya gudanar da wanann zaman taro, ya bayyana cewa babbar manufarsu ita ce isar da fahimta kan muslunci ga mutanen Amurka, musamamn ma irin wannan yanayi da ak ena rashin ganij kimar musulmi.
Ya ce adadin musulmin kasar ya kai miliyan 5 zuwa 7, kuma daga cikinsu akwai manyan injiniyoyi da kuma manyan likitoci da ake takama da su a kasar, amma saboda mummunan farfaganda kan muslunci, hakan yasa ana yi musu wani kallo na daban.
Ya kara da cewa addinin muslunci yana girmama dan adam, musulmi ko ba musulmi ba, ko bayahude ko kirista koma wane addini yake bi, kuma musluci a kowane lokaci a shirye yake ya yada fahimtar juna a tsakanin al’umma da zaman lafiya.
Sakamkon abubuwan da suke faruwa a duniya na ta’addanci da sunan addinin muslunci, hakan ya sanya ana bayar da mummunar fahimta da fassara ga muslunci da kuma addinin muslunci a duniya, wanda hakan ya yi tasiri musamamn ma a tsakanin Amurkawa.