IQNA

An Zabi Sabbin Makaranta Kur’ani Na Masallacin Azhar

23:47 - March 29, 2016
Lambar Labari: 3480271
Bangaren kasa da kasa, an zabi sabbin makaranta kur’ani mai tsarki guda 7 da za su rika yin karau a babban masallacin Azhar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na innfrad.com cewa, Muhammd Muhanna babban mai kula da masallacin cibiyar Azahar ya bayyana cewaan zabi makaranta guda 7 da nufin samar da yanayin sahihin karatu a masallacin.

Ya ce kafin daukarsu duk sai aka yi musu jarabawa kuam suka dace sa’annan aka dauke su.

Muhamamd Muhanna ya kara da cewa, daukar makarnta yan kasar Masar ad kuma ‘yan kasar waje yana da matukar tasiri wajen kyautata yanayin da ake bukata a wanann babbar cibiya ta duniya.

Ya ce akwai bukatat samar da yanayi na karatun kur’ani wanda kowa zai shiga a cikinsa, da hakan ya hada da salo irin na Masar da kuma salon a wasu kasashen msuulmi da na larabawa, domin kowane bangare a bashi hakkinsa awannan babbar cibiya ta muslunci.

Haka na kuma ya kara da cewa daga cikin wadanda aka zaba akwai malaman kur’ani daga biranan Masar wadanda za su rika koyar da karatun kur’ani da ilmominsa a masallaci, domin amfani masu halarta.

3484817

captcha