
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, a ranar 20 ga watan Oktoban shekara ta 2015 ne mahukunta a Bahrain sun kame sheikh Abdulzahra Almubasshir sakamakon wani jawabi da ya gabatar a ranar Ashurar Imam Hussain (AS).
Babbar kotun kolin masarautar kasar tace malamin yana yin jawabi wanda zai iya sanyawa mutane su kyamaci mahukuntan kasar.
Kama sheikh Almushir dai ba shi ne na farko ba, domin tun kafin wannan lokacin an kame malami da masu fafutukar kare kare hakkokin bil adama akasar duk bias irin wannan tuhuma.
Babbar manufar sarakunan Bahrain dai ita ce hana duk wani yunkurin da zai kai ga al’ummar kasar ta samu yancinta na siyasa da kuma hakkokinta na kasa.