IQNA

Shiri Kan Matsayin Wilayat Faqih A Talabijin A Kasar Ghana

17:30 - March 31, 2016
Lambar Labari: 3480277
Bangaren kasa da kasa, an gudabnar da wani shirin talabijin a kasar Ghana kan matsayin wilayat Faqih a jamhuriyar muslunci ta Iran.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adun muslunc cewa, a jiya ne aka gudabnar da wani shirin talabijin a kasar Ghana kan matsayin wilayat Faqih a jamhuriyar muslunci ta Iran wanda malam Idris Tupo ya gabatar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannans hiri dai cibiyar kula da yada al’adun muslunci ta jamhuriyar muslunci ta Iran ce ta dauki nauyin gudanar da shi, inda tashar talabijin ta TV home bau ta dauki nauyin watsawa, inda aka yi bayani kan matsayin jagorancin malami wanda Marigayi Imam Khomeni (RA) ya kafa akasar Iran tun bayan samun nasar juyi.

Tare da bayyana matsayin Iran kan abubuwan da suke wakana a yankin gabas ta tsakiya da kuma tsayin Iran a kansu, musamamn ma a Bahrain, da Syria, da kuma kasar Yemen.

Haka nan kuma an yi baynai kan gudunmawar da jagora yake bayarwa wajen ganintsarin da Imam Khomei (RA) ya kafa ya ci gaba da tafiya, tare da bayyana cewa irin wanann tsari na shugabancin malami yana da babban tasiri a fagage da daman a zamantakewar al’umma musulmi, domin kuwa ana kare hakkokinta na musulunci da kuma yan adamtaka baki daya.

3485019

captcha