IQNA

Ministar Mata A kasar Faransa Ta Yi Cin Zarafi Ga Musulmi

17:34 - March 31, 2016
Lambar Labari: 3480279
Bangaren kasa da kasa, Larance Rosinal ta ci zarafin mata musulmi a kasar Faransa sakamkon saka hijabin muslunci da suke yi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafi sadarwa na yanar gizo na Aljazeera cewa, wanann minister ta yi cin zarafin ne alhali tana a cikin majalisar ministocin kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa ta bayyana mata musulmi a mtsayin cewa suna daidai da bayi da aka kai kasar Amuka bakaken fata domin su yi bauta.

Baya ga haka ma ta yi cin zarafi ga su kansu bakaken fata bai daya, inda take kamanta su da coco, tana mai cewa a lokacin da aka dauki bakaken coco zuwa Amurkaka bautar da su, tana mai cewa da su da musulmi duk abu guda ne.

Wannan furuci dai ya jawo martini mai kaushi daga al’ummomin kasar Faransa, inda ya zuwa yanzu haka kimanin mutane 10,000 ne suka rattaba hannu kan wata wasika da ke nemana gaggauta tsigeta, saboda wannan mummunan furuci da ya fito daga bakinta.

3485017

captcha