IQNA

Horo Kan karatu Da Hardar Kur’ani A Tsibirin Komoros

23:39 - April 08, 2016
Lambar Labari: 3480302
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani shiri na bayar da horo ga dalibai 89 na koyon karatu da hardar Kur’ani a Komoros.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewam ya nakalto daga shafin sadarwa na gulfeyes.net cewa, a jiya ne ka kammala wani shiri bayar da horo kan kur’ani na kwanaki 50 a tsibirin na Komoros a karkashin cibiyar kur’ani ta Sa’ad bin Mu’az.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri an gudanar da shi a cikin nasar, tare da samar da yanayi mai matukar muhimmanci a bangaren hardar kur’ani da karatunsa.

Koyon hardar kur’ani da tajwidi da kuma tilawa suna daga cikin muhimman abubuwan da shirin ya kunsa gami da adduoi da zikirori.

A lokacin gabatar da taron rfe shirin, an samu halartar daruruwan mutane da suka zo, da suka hada da jami’ai da kuma malamai gami dsa musulmi mutanen gari.

An gabatar da laccoci da kuma yin bayani kan muhimamncin karatu da hardar kur’ani mai tsarki a tsakanin al’ummar msulmi, da kuma sanin yadda ya kamata akara karfafa hakan.

Bayan gabatar da jawabai an bayar da kyautuka ga wadanda suka halarci ewanann shiri, musamman ma dai wadanda ska yi kwanaki suna koyon abin aka bayar da horo a kansa.

Tsibirin Komoros dai yana d cikin tsibirrai na gabashin nahiyar Afirka, kuma yana daga cikin mambobin kungiyar kasashe larabawa.

3486617

captcha