IQNA

Baje Kolin Kur’ani Na Digital A Dakin Karatun Birtaniya

23:40 - April 08, 2016
Lambar Labari: 3480303
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani baje koki na dadadden kwafin kur’anai a babban dakin karatu na Birtaniya da ke komawa zuwa ga karni na kwas.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alarabi Jadid cewa, wannan kwafin kur’ani mai tsarki an rubuta shi da hannu a cikin shafuka 121, wanda kuma yana dauke da kusan kasha daya bisa uku na cikakken kur’ani.

Bisa ga bayanan da aka samu daga wannan babban dakin tarihi na Growell John Chester an rubuta wannan kwafin kur’ani nea cikin shekara ta 1879, kuma an sayo shi a tsakanin 1830 zuwa 1892.

Growell John Chester wani malmin addinin kirista ne, kuma masani kan harkokin tarihi wanda yake da matukar bincike da kauna kan abubuwa da suka shafi tarihi, a kan haka ya yi tafiya zuwa Masar a lokuta da dama, inda ya tara littafai da kayan tarihi da ya saya a can, inda ya kafa babban dakin kayan tarihi.

Wannan dakin tari kafin wannan lokacin ya nuna wani kur’ani na tarihi, wanda ak arubuta a tsakanin shekarun 1304 zuwa 1306, wanda yake da alaka da sarakunan da suka gabata, wadanda suka yi mulki a kasashen msuulmi a lokacin.

Dakin karatun na Birtaniya da aka fi sani da (The British Library) shi ne dakin karatu mafi girma aduniya, kuma yana a birnin London.

3486614

captcha