
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Plastinu cewa, Sheikh Raid salah ya kirayi dukaknin palastinawa mazauna birnin Quds, da su gaba da yin zaman dirshana cikin masallacin Aqsa mai alfarma.
Ya ce yahudawamn sahyuniya suna shirin keta alfarmar wannan masallaci da sauran wurare masu tsarki da ke wurin, kuma nauyin kare wannan wuri ya rataya kansu.
Sheikh Raid salah y ace san cewa jami’an tsaron yahudawan sahyuniya sun dauki kwararan matakan tsaro, amma duk da haka palastinawa su dage a kan kare wrarensu masu tsarki.
Jagoran harkar muslunci a Palastinua cikin yankuna 1948 ya bayyana cewa, yahudawa suna da shirin gudanar da bukukuwansu na idi a cikin wannan masallaci mai alfarma, saboda haka za su ci gaba da kasancewa a cikin masallacin domin hana afkuwar hakan.
Tunb a yau ba dai yahudawa suna ta kokarin ganbin sun keta alfarmar wannan masallaci mai tsarki, ta hanyar rusa shi ko kuma yin gini ta karkashinsa domin ya rufta.