Kamfanin dillancin labaran Iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin ya
habarta cewa, kashi 5.9 zuwa kasha 27 na mata musulmi ne bas u da aikin
yia Birtaniya, yayin da wadanda ba
musulmi kasha 3.7 ne kawai a kasar.
Sakamakon ya nuna cewa hatta a bangaren aiki da ake bukatar kwarewa, mata msuulmi suna samun kashi 23 ne kawai, yayin da wadanda ba msuulmi ba suke samu kashi 32 cikin dari.
Haka nan kuma sakamakon ya nuna cewa wannan banbancin yana nan ko da kuwa ta fuskakacin karatu da ilimi babu banbanci tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi, amma ana fifita wadanda ba musulmi ba a kasar.
Wannan bincike dai Nabil Khitab ne tare da Shirin Husain daga College King da ke birnin London ne suka gudanar da bincike tare da taimakon wasu cibiyoyi, kuma bincike ya shafi mutane kimanin rabin miliyon.
An bayyana sakamakon bincike n a taron kara wa juna sani kan ilimin zamantakewa a birnin London.
Babban abin da ake fara dubuwa wanda kuma shi ne yake jawo wa msuulmi bakin jinni a kasar shi ne saka kayan muslunci da rufe jiki da suke yi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kyamar msuulmi a birnin Landan ya karu kashi kimanin 70 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.