Kamfanin dilalncin labaran kur’ani
na Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na QAF cewa,
wannan shiri ana gudanar da shi ne
karkashin kulawar cibiyar da ke kula da hubbaren Abul Fadl Abbas (AS) a ofishin
cibiyar Nur da ke Landan.
Manufar taron dai ita ce hada malamai masu koyar da karatu da sauran ilmomin kur’ani mai tsarki kan wani tsari guda na koyarwa.
Babban malami sheikh Diya Zubaidi shi ne shugaban wannan cibiya da take da alaka da cibiyar hubbaren Abbas (AS).
Dukkanin mahalarta wannan taro dai sun hadu a kan wajabcin mayar da hankali matuka wajen ganin an kyautata tsarin koyar da karatun kur’ani mai tsarkia makarantun muslunci, domin samar da al’umma masaniya kan kur’ani mai tsarki da kuma ilmominsa.