IQNA

Jagoran Juyin Islama:

Dole Ne Kasashen Musulmi Su Yi Tare Da Juna Da Gaskiya

20:23 - April 12, 2016
Lambar Labari: 3480315
Bangaren siyasa, a lokacin da ya yake ganawa da shugaban kasar Kazakhstan jagoran juyin Islama Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, ya zama wajibi kan kasahen musulmi su yi aiki tare da gaskiya domin ci gaban kasashensu da al’ummominsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yammacin yau Litinin ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaban kasar Kazakhtan Nursultan Nazarbayev da 'yan tawagarsa da suka kai masa ziyarar ban girma, inda yayin da yake ishara da wajibcin kara karfafa irin alakar da ke tsakanin kasashen biyu a fagage daban-daban na siyasa, tattalin arziki, kasa da kasa da kuma fada da ta'addanci ya bayyana cewar: wasu daga cikin manyan kasashen duniya musamman Amurka, ba da gaske suke yi ba cikin ikirarin fada da ta'addanci da suke yi. To amma kasashen musulmi za su iya kawar da wannan barazana ga duniyar musulmi ta hanyar aiki tare da gaske a tsakaninsu.

Ayatullah Kahmenei ya bayyana taimakon da Amurkawa suke ba wa kungiyar Da'esh a kasar Iraki a matsayin daya daga cikin misalan rashin gaskiyar hadin gwiwan kasashe daban-daban da suke ikirarin fada da ta'addanci inda ya ce: Don halalta irin wannan mu'amalar harshen damo da suke yi ne ya sanya su raba ta'addanci zuwa nau'oi biyu mai kyau da mara kyau.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da 'yan kasashen Turai daban-daban da ake samunsu da hannu cikin ayyukan ta'addanci a kasashen Turan haka nan kuma da yadda ake samun wani adadi mai yawan gaske na wadannan mutane cikin kungiyoyin 'yan ta'addan da suke gudanar da ayyukan ta'addanci a kasashen Siriya da Iraki, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Hakan wani lamari ne da ke nuni da rashin gaskiyar kasashen yammaci musamman Amurka a fadar da ake yi da ta'addanci a duniya.

Jagoran ya bayyana halin da ake ciki a halin yanzu a duniya da cewa wani yanayi mai tada da hankali da kuma rashin tabbas inda ya ce: A halin yanzu dai duniyar musulmi tana fuskantar barazanar kungiyoyin ta'addanci wadanda suke gudanar da ayyukan ta'addancinsu da sunan Musulunci a kan musulmi, sannan a bangare guda kuma wasu daga cikin manyan kasashen yammaci ba sa kaunar ganin kasashen musulmi sun hada kansu waje guda.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar fada da barazanar ta'addanci da kuma mu'amalar harshen damo ta manyan kasashen duniya lamari ne da ya sanya kara karfafa alaka da aiki tare tsakanin kasashen musulmi ya zama wajibi inda ya ce: Mu dai muna daukar kasashen musulmi a matsayin 'yan'uwanmu, sannan kuma mahangar Iran da Kazakhstan sun zo daya a mafi yawa daga cikin batutuwan da suke gudanar a duniya.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da alaka da aiki tare da ke tsakanin kasashen Iran da Kazakhstan a fage na kasa da kasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Duk da irin kusaci na addini, tarihi da kuma al'adu iri guda haka nan kuma da kuma fagage daban-daban da kasashe biyun suke da su, to amma alaka ta kasuwanci da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu tana kasa kasa. A saboda haka Iran tana maraba da karfafa alaka da aiki tare tsakanin kasashen biyu a fagage daban-daban da sukahada da siyasa, tattalin arziki, kasuwanci, sufuri, haka nan kuma da hakkokin da ake da su a Tekun Caspian.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Kazakhtan Nursultan Nazarbayev wanda shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani yake wa jagoranci, ya bayyana kasar Iran a matsayin babbar makwabciya kana kuma abar dogaro da kuma yarda inda ya ce: Kasashen biyu suna da fagage da dama da za su iya amfani da su wajen fadada alakar da ke tsakaninsu. A saboda haka ne a yayin wannan ziyarar mun cimma yarjejeniyoyi masu muhimmanci wadanda za su taimaka wajen ciyar da alakar da ke tsakanin kasashen biyu gaba.

Shugaban kasar Kazakhtan ya bayyana ta'addanci a matsayin babbar barazana, haka nan kuma yayin da yake ishara da faruwar ayyukan ta'addanci a kasashen yammaci da kuma kokarin da suke yi na bayyana addinin Musulunci a matsayin wani tushe na ta'addanci ya bayyana cewar: A hakikanin gaskiya ayyukan ta'addanci da kuma matsalar 'yan gudun hijira da ake fama da su sun samo asali ne sakamakon fada da halaltattun gwamnatocin yankin nan da kasashen yammaci suke yi. Don kuwa a duk lokacin da aka kawar da wata halaltacciyar gwamnati a wata kasa, to kuwa ta'addanci ne zai maye gurbinta.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu bugu da kari kuma kan irin tasirin da Jagoran juyin juya halin Musulunci yake da shi a kasashen musulmi, shugaban Nazarbayev ya bayyana cewar: Lalle ni na yi na'am da mahangarka dangane da batun hadin kan kasashen musulmi. Wajibi ne mu nuna wa dukkanin duniya cewa addinin Musulunci, addini ne na ci gaba, hadin kai da kuma fada da ta'addanci.

3487758

captcha