
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin ISESCO cewa, kungiyar za tagudanar da wani zaman taro domin bin kadun cin zarafin musulmi da wulakancin da ake yi musu tun bayan faruwar kai harin Brusselsna Belgium, kuma za a yi hakan ta hanyar wasu kotuna.
Bayanin y ace a cikin kwanaki uku masu zuwa ne za a gudanar da zaman taron.
Tun bayan kai wannan hari dai mabiya addinin muslnci suna fuskantar matsaloli da dama a cikin wasu kasashen yammacin turai, da hakan ya hada har da wasu birane na kasar ta Belgium da aka kai garin.
Wasu daga cikin masu tsatsauran ra’ayin kiyayya da musulunci a cikin kasashen turai, sun jima suna ta kokarin samun wata dama da za su ci zarafin musulmi, wadannan hare-haren da ‘yan ta’adda suke kiwa sun zam ababban lasisi gare su domin cin zarafin musulmi.
Wannan taro da za a gudanar dai zai mayar da hankali ne kan yadda za a dauki matakai na shara’a domin hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen cutar da musulmi da suna daukar fansa kansu dangane da ta’addanci.
Daga cikin abubuwan da suka wakana cikin yan kwanakin nan na cin zarafion musulmi har dai kai hari kan masallatai da makarantu.
Kugiyar bunkasa harkokin al’adu da ilimi ta duniya ta sha alwashin daukar matakai na kare musulmi ta hanyar dokokin da ake amfani da su a cikin kasashen turan domin kwato musu hakkokinsu.