Kamfanin dillancin labaran quran na
Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Jaridar Yaum Sabi ta
bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da shehin malamin ya fitar a jiya
Talata, ya ja kunnen yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayi da ke shirin
shiga cikin masallacin Quds, domin gudanar da bukukuwansu na shekarar yahudawa
a cikin masallacin mai alfarma.
Sheikh Muhammad Hussain ya ce yin hakan na nuna cewa akwai alamar yaki na addini ya barke a tsakanin musulmi da yahudawa a Palastinu, domin kuwa musulmin Palastinu ba za su taba amincewa da keta alfarmar masallacin Quds alkiblar musulmi ta farko ba,a daidai lokacin da dubban yahudawa ke shirin shiga cikinsa domin yin bukukuwa, wadanda suke samun kariya daga daruruwan jami'an tsaron Isra'ila.
Daga Karshe Sheikh Muhammad Hussain ya kirayi al'ummar musulmi da ta saufke nauyin da ya rataya a kanta ta hanyar taka birki ga yahudawan sahyuniya, dangane da keta alfarmar wurare masu alfarma na musulmi da suke yi a cikin yankunan palastinu baki daya, da hakan ya hada har da masallacin Quds.