Kamfanin dilalncin labaran iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewa,
babban mai bayar da shawar ga Shehul Azahar y ace an fara gudanar da dukkanin
shirin fara wannan gasa a cikin watan azumi mai zuwa.
Ya jaddada cewa wannan gasa dai za a gudanar da ita ne tare da sanya ido na babban malamin Azahar Ahmad Tayyib.
Gasar dai ana gudanar da ita ne mataki mataki, inda wasu sukan barta tun daga matakin farko bayan an fitar da su wasu kuma za su wuce zuwa mataki nag aba.
Mahanna y ace an zabi watan Ramadan mai alfarma domin gudanar da wannan gasa mai matukar muhimmanci, inda manyan malamai da jami’ai na kasar suke taruwa domin halartar gasar.
Y ace ga dukaknin wadanda suke da bukatar shiga cikin wannan gasa za su iya yin rijistar sunayensu ba tare da wani bata lokaci, domin a saka sunayensu a cikin jerin masu shiga gasar.
Haka nan ya kuma ya kara da cewa, tsawon kwanaki goma sha biyar ne kawai ake bayarwa domin yin rijistar masu shiga gasar, inda yanzu haka an fara.