IQNA

Makarancin Kur’ani A Masallacin Annabi (SAW) Ya Rasu

23:30 - April 16, 2016
Lambar Labari: 3480329
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Muhammad Ayyub makarancin kur’ani mai tsarki a masallacin manzon Allah (SAW) ya rasu a yau.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Alriyad cewa, , Sheikh Muhammad Ayyub makarancin kur’ani mai tsarki kuma limami a masallacin manzon Allah (SAW) ya rasu yana da shekaru 68 da haihuwa.

Dan Sheikh Muhammad Ayyub ya bayar da labarin cewa mahaifin nasa ya rasu a shafinsa na yanar gizo na Twitter, kuma y ace za agudanar da janazarsa a makabartar Baki’a da ke Madina.

An haifi Mhammad Ayyub a cikin shekarar 1372 H a garin Makka kuma ya yi karatu a hannun Zaki Dagistani, da Sheikh Khalil, inda ya yi harda, daga nan kuma ya yi karatu a hannun Muhammad Abdulaziz Usaman, da Akram Diya Alumri, sai kuma Muhamamd Amin Shaqiti, da Abdulmuhsin Al-ibad.

Ya dais hara da sunan sheikh kurra, saboda kasantuwarsa yana bayar da salla da kuma karatun kur’ani a masallacin annabi.

Haka nan kuma ya yi sunan ta fuskar karatun kur’ani da kyautata sautinsa, inda yak an jagoranci sallar ashama ckin watan azumi, kuma ana saka karatnsa a cikin gidajen radio na kasar.

3489060

captcha