Bayanin y ace ya zuwa yanzu dai an kamala izihin surat amma, wato juzu'I na 30, kuma a cikin mako mai zuwa da yardarm Allah za kamala juzu'in 29.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan aiki yana daya daga cikin irinsa da aka fara, wanda kuma ya samu karba daga al'ummar kasar.
Raniya Aliyu da Sahar Abdulmuhsin su ne masu kula da dakin gudanar da wannan aiki na fasaha.
Shi ma a nasa bangaren Shu'aib khalaf babban daraktan ma;aikatar kula da harkokin al'adu a jahar Alminya ta kasar Masar ya bayyana wannan aiki na fasa da cewa yana da matukar muhimamnci wajen kara fito da matsayin addini.
Ya ce bayan kamala aikin baki daya za su alluna na dukkanin abubuwan da aka rubuta domin saka su a gidan tarihi na kasar, wanda hakan zai zama wani babban abin alfahari ga al'ummar kasar Masar baki daya.
A nasa bangaren shi ma Fathi Idris shugaban cibiyar rubutun larabci ta kasar wanda ya halarci, ya bayyana jin dadinsa matuka, musamman ma ganin cewa abin da ake yi zai amfani al'ummar msuulmi da kuma larabawa baki daya.
Tare da yin fatan ganin cewa wanan aiki da aka fara dore, ya zama a bin koyi ga sauran masu rubutun fasaha na larabci a kasar da ma sauran kasashen larabawa da na musulmi.