Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bhabarta cewa ya nakalto daga
shafin sadarwa na yanar gizo na Ma'a cewa, a karon farko an gudanar da wani
zaman taron karawa juna sani da bita a Gaza kan rayuwar Ibn Aljazari wanda aka Haifa
a cikin shekara ta 751 – 833 a jami'ar Sahabah.
Wannan zama dai ya gudana ne a babban dakin taruka na jami'ar sahabah da ke yankin Nusairat a Gaza, tare da halartar malaman addini da dama.
Marwan Abu Ra'as shugaban bangaren bincike na jami'ar ya bayyana cewa, wannan taro yana da matukar muhimmanci musamman a wannan zamani da ake bukatar Karin bayani kan irin wadannan mutane.
Ya ce wannan malami yana daya daga cikin manyan malamai da aka yi, wanda karatunsa yake da matukar tasiri a cikin zukatan masu saurarensa.
Muhammad Bin Yusuf Aljazari Al-damashki an haife shi a cikin shekara ta 751 Hijiriyyah, kuma ya hardace kur'ani tun yana da shekaru 13 da haihuwa a duniya.
Ana yi masa lakabi da Sheikhul kurra saboda matsayinsa na ilimin kur'ani da karatunsa, ya kuma kware a bangarorin tafsiri, Tauhidi, Usul, Hadisi, Sarf, Balga, Nahwu da sauransu, kuma ya yi rubutu a dukkanin wadannan bangarori.