IQNA

Taron Karawa Juna Sani Kan Kur’ani Mai Tsarki A Yemen

22:29 - April 18, 2016
Lambar Labari: 3480334
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan lamuran kur’ani a jami’ar Abb da ke kasar Yemen.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Gulfeyes.net cewa, Tarik Almansub shi ne shgaban jami’ar Abb takasar Yemen shi ne kuma babban bako a wurin taron wanda aka shirya awannan jami’a.

A wurin taron an gabatar da jawabai da suka danganci kur’ani da yadda ya kamata a kara habbaka ilmomin kur’ani mai tsarki a cikin kasashen msuulmi, wanda kuma bangaren nazari kan kur’ani a wannan jami’a na yin kokari ta wannan fuska.

Daga cikin jawaban da aka gabatar a wurin, akwai kira ga al’ummar msuulmi kan su mayar da hankali zuwa ga koyarwar kur’ani da nufin warware matsaloli na rashin fahimtar juna da rikici a tsakaninsu.

Bayanan sun mayar da hankali kan ilmantar da sauran musulmi dangane da yadda ya kamata su fuskanci kalu balen da ke gabansu da kuma yadda makiya suke hankoron ganin sun rusa al’ummar musulmi.

Dag ciki kuwa har yadda wasu kasashen da ke wa makiya aiki da sunan addini suke amfani da akidarsu wajen rusa muslunci, musamman ma wasu daga cikin kasashen da ke tinkaho da cewa suna kare sunna, inda su ne kan gaba wajen kare manufopfin yahudawa akasashen muslu.

Babban misalign hakan shi ne yadda wadannan kasshen suka kaddamar da yaki kan al’ummar musulmi na kasar Yemen, inda suke kashe dubban mutane musulmi maza da mata da kanann yara da rusa masallatai.

Wanda hakan ya zama wajibi a wayar da kan musulmi kan hakikanin koyarwar kur’ani da kuma banbance tsakanin musulmi na kwarai da kuma munafukai baragurbi.

Jmai’ar Abb dai an gina ta ne a cikin shekar ta 1996, kuma tana daya daga cikin manyan jami’oin kasar a halin yanzu da suke mayar da hankali kan ilmomin zamani da kuma na addini.

3489641

captcha