Kamfanin dillancin labaran Iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na arabesque.tn cewa, Muhammad Khalil ministan harkokin addini na
kasar ta Tunisia ya bayyana cewa, daga yanzu makarantun
kasar Tunisia za su rika koyar da yara karatun kur’ani mai tsarki a ranakun da
ake hutu a kasar.
Ya ce wannan zai taimaka matuka ga yara da ba su samun samar yin karatu a lokutan htu su yi amfani da wannan damar domin koyon karatun kur’ani mai tsarki da kuma koton wasu daga cikin ilmominsa.
Ministan ya ce wannan duk yana a karkashin shirin da suke da shin a yaki da ta’addanci ta hanyar koyar da hakikanin koyarwar kur’ani mai tsarki ga kananan yara.
Tun a cikin watan da ya gabata ne ma’iakatar kula da harkokin addini ta kasar Tnisia ta sanar da bullo da wani shiri na yaki da ta’addaci ta hanyar wayar da kan yara.
Bayanin ya ce alkur’ani mai tsarkidai shi ne hanyar koyar da yara akidar muslunci dsahihiya, maimakon yadda wasu suke amfani da shi wajen karkatar da tannin matasa daga cikin musulmi zuwa ga ayyukan ta’addanci.