IQNA

An Saka Furanni A Hubbaren Amirul Muminin (AS)

23:36 - April 20, 2016
Lambar Labari: 3480340
Bangaren kasa da kasa, an saka furanni a dukkanin sassa nan a hubbaren Imam Ali (AS) a daidai lokacin da ake tunawa da ranar haihuwarsa mai albarka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga bangaren yada labarai na hubbaren Alaw cewa, a daidai lokacin da ake shirin gudanar da taron zagayowar ranar 13 ga Rajab ranar haihuwar Imam Imairul muminin (AS) masu hidima a wannan hubbare mai tsarki sun saka furanni a koina.

Haka nan kuma bisa ga wannan lokaci na zagayowar wannan rana mai albarka, an daga tutoci a koina gefen hubbaren mai tsarki.

Haka na kuma a gobe idan Allah ya kai mu za araba furanni guda dubu 6 ga masu ziyara a wannan wuri mai albarka, kamar dai yadda aka saba gudanarwa.

3490546

captcha