
Kmafanin dillanicn labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na Al-nashrah cewa, Kotun daukaka kara a kasar Mauritaniya, ta kara tabbatar da hukuncin kisa a kan Muhammad Sheikh Wuld Ummu-khaitir, wanda ya rubuta wata makala a shekara ta 2014, kuma a cikin makalar ya ci zarafin fiyayyen halitta manzon tsira Muhammad (SAW) a garin Nawadibo.
Tun kafin wannan lokacin dai kotun kolin kasar ta Mauritaniya ta bukaci da a tabbatar da wannan hukunci a kan wannan mutum wanda ya yi batunci ga manzon Allah (ASW) wanda kuma kotun daukaka kara akasar ta yi nazari kan hakan kuma ta kara tabbatar da hukuncin.
Babbar kotun kolin ta ce hakan yana da matukar muhimmanci domin ya zama darasi gay an baya da ma duk wani yake tunannin cewa zai iya cin zarafin manzon Allah (SAW) a kasar ya kwana lafiya.
Muhammad Sheikh Wuld Umkhaitir dai ya nemi afuwa bisa ga abin da ya aikata, inda y ace ya yi kuskuren fahimta ne kan wasu ayoyin kr’ani wadanda daga baya ya gane cewa shi ne ya yi kure.
Wannan neman hanzari dai bai samu karbuwa, domin kwa tun daga lokacin da ya yi wannan rubutu a cikin 2014, ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman yank e hukuncin kisa akansa a fadin kasar.
Wannan hukuncin kisa da aka yanke masa wanda ake ta yin kira akansa a kasar tun daga shekara ta 2014, ya samu karbuwa daga al’ummar kasar.