IQNA

An Dage Taron Kur’ani Da Aka Shirya Gudanarwa A kasar Morocco

23:51 - April 22, 2016
Lambar Labari: 3480348
Bangaren kasa da kasa, an dage zaman taro kan mujizar kur’ani da sunna da aka shirya gudanarwa akasar Morocco.

Kamfanin dillanicn labaran iqn aya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bledna.com cewa, majalisar malaman addini ta garin Khabika a kasar Morocco ta sanar da dage taron har zuwa ni lokaci a nan gaba.

Bayanin da majalisar malaman ta fitar ya ce daukar wannan mataki dai ya zo ne sakamakon rashin kammala shirin da ya kamata domin daukar nauyin gudanar da wanann taro.

Amma a cewar bayanin da zaran an kammala dukkanin shirin da ya kamata za a sanar da dukkanin kasashen da za su halarta domin gudanar da taron kamar yadda ya kamata.

Majlaisar malaman addinin muslunci ta garin Kharbika ta ce za a gudanar da wannan zaman taro ne a jami’a Sidi Muhammad Abdullah, wadda day ace daga cikin manyan jami’oi na addini a kasar.

Daga cikin kasashen da aka shirya cewa za su halarci wannan zama a kwai ita kan Morocco, Saudiyya, UAE, Kuwait, Aljeriya, Masar, da kuma Iraki.

Daga cikin muhimamn abubuwan da wannan taron ke mayar da hankalia kansu kwai batun ilimin kur’ani a bangarori na balaga da salon sajai da kuma kololowar hikimar Magana, wadda Magana ce amma da tsari wand aba na waka ba, ta banbanta da tsarin Magana ta yau da klum da mutane suke , da ma wasu abbuwa da ska shafi kr’ani da ake karawa juna sani a kansu.

3490923

captcha