IQNA

Gasar Karatu Da Hardar Kur’ani Ta Kasa A Algeriya

23:27 - April 23, 2016
Lambar Labari: 3480349
Bangaren kasa da kasa, an bude gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a kasar a babban ginin cibiyar Darul Imam a birnin Algiers.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «radioalgerie.dz» cewa, a yau an bude gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a kasar a babban ginin cibiyar Darul Imam a birnin Algiers tare da halartar ministan kula da harkokin addini Muhammad Isa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa da aka bude ta kasa baki daya a fadar mulkin kasar ta Algeriya tana daga cikin muhimman gasar da ake gudanarwa a kasar a halinyanzu, wadda wannan ita ce karo na shida.

Ministan kula da harkokin addini a kasar ta Algeriya ya bayyana agaban taron cewa, wannan babban abin farin ciki ga al’ummar kasar baki daya.

Ya ce mayar da hankali ga lamurra da suka shafi koyarwar kur’ani mai tsarki a tsakanin al’umar kasar shi ne yafi komai muhimmanci, domin kuwa kasar Algeriya kasa ce ta musulmi, kuma masu koyi da kur’ani mai tsarki.

Haka nan kuma ya kara da cewa gudanar da gasar kur’ani na da muhimmanci wajen kara karfafa gwiwar matasan musulmi wajen mayar da hankali ga kur’ani mai tsarki, a kan za a ci gaba da gudanar da wannan gasa da yardarm Allah.

Abin tuni a nan dais hi ne, wannan gasa ta kasar Algeriya ana gudanar da ita a mataki na kasa baki, inda wakilai daga cibiyoyin addini da makarantu daga dukkanin jahohin kasar suke taruwa a babban birnin kasar domin halartar wannan gasa, kuma lamarin yana ci gba da kara bunkasa akowace shekara.

3491005

captcha