IQNA

Gasar Kur’ani Ta Kasar Morocco A Watan Ramadan

23:25 - April 24, 2016
Lambar Labari: 3480352
Bangaren kasa da kasa, a cikin watan Ramadan mai alfarma ne za a gudanar da bangaren gasar kur’ani ta sarki Muhammad na 6 a kasar Morocco a birnin Ribat.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «nadorcity.com» cewa, watan Ramadan mai alfarma ne za a gudanar da bangaren gasar kur’ani ta sarki Muhammad na 6 a kasar Morocco a birnin Ribat a masallacin Sunnah.

Bayanin y ace wannan gasa tana daga cikin irinta masu matukar tasiri da ake gudanarwa akasar, domin kuwa tana hada dukkanin bangarori na kasar a wuri guda domin gudanar da gasa.

Mataki na karshe na gasar dai yana da bangarori da suka kebanci harda da kuma karatu kur’ani tartili, sai kuma bangaren sanin kaidojin karatu da hukuncinsa na Tajwidi, wanda kuma bangaren an karashe zai gudana a masallacin Alfath da ke yankin Al-nazur.

Tun farkon bude gasar dai an gudanar da taron ne a garinna Nazur, inda makaranta maza da mata suka halarci gasar kuma suka bayar da gudunmawarsu.

Kimanin makaranta da mahardata 200 ne dai suka samu damar kaiwa ga mataki na karshe na wannan gasa, kuma daga cikinsu za a fitar da matakan da ake bukata na daya da na biyu da kuma na uku.

Daga karshe kuma za a bayar da kyautuka na tukuici ga wadanda suka nuna kwazoa dukkanin matakai, inda za a yi taro na rufewa tare da girmama su da kuma halartar manyan jami’an masarautar kasar da kuma na gwamnati.

3491499

captcha