IQNA

America pure: Iayalai Masu Da Addinin Sun Fi Nishadi

23:28 - April 24, 2016
Lambar Labari: 3480353
Bangaren kasa da kasa, wani bincike da aka gudanar a kasar Amurka ya nuna cewa iyalai masu kuladsa addini sun fi nishadi a tsakanin al’ummar kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «World Religion News» cewa, wannan binciken an gudanar da shine bisa taken mutanen Amurka da suka fi nishadi.

Sakamakon wannan bincike dai ya nuna cewa, wadanda suke riko da addini ba tare da la’akari da addini da suke bi ba, su ne suka fi kowa za a cikin nishadi su da iyalansu.

Wannan jin ra’ayin jama’a dai angudanar da shi ne a tsakanin al’ummar kasar a birane daban-daban domin hada sakamko wanda zai dace da yanayin kasar baki daya.

Daga cikin iyalan da aka ji ra’ayoyinsu, wasu ana samun mas addini, wasu kuma bas u da kulawa kan addini, kamar yadda kuma marassa kula da addinin su ne suka fi yawa, kuma su ne suka fi yawan aikata ba dadidai ba.

Kamarv yadda kuma wadanda suke da addini su ne suka fi kula da rayursu ta zamanewa tsakaninsu da al’umma, kamar yadda kuma su ne suka fikula da iyalansu tare da kyuatat suu da nuna musu kyawawan dabiu.

Mabiya addinin muslunci a kasar Amurka dai su ne marassa rinjaye, kuma a duk inda suke da cibiyoyinsu sukan fita daban, kuma sukan zama abin buga misali da su wajen kyawawan dabi, wanda hakan ke kara tabbatar da cewa muslunci addini ne na kyawawan dabiu da zaman lafiya da al’umma.

3491512

captcha