
Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na iidr cewa, wannan shiri zai fara ne a cikin watan gobe.
Bayanin ya ci gaba da cewa uhimman abubwan da za amayar da hankali a kansu shi ne matsayin watan azumi a wurin musulmi, da kma yadda ya kamatra su karbi wannan wata mai alfarma.
Daga ciki kuwa har yadda ya kamata su rika gudanar da lamurra na ibada da kuma sauran lamurran zamantakewa, domin kuwa wata ne mai matsayi na musamman a wajen ubangiji.
Kamar yadda kuma matsayinsa a wajen ubangiji ne ya sanya shi ya zama mai albarka, wanda ibada a cikinsa take da matsayi na musamman wanda yake mafifici a kan sauran lokuta wadanda ban a cikin wannan ba.
Muhammad fars wani matashi ne muuslmi mazaunin kasar, kuma ya kasance a cikin masu halartar wannan shiri da suke jagorantarsa, ya babbayana acewa a shekarar bana mutane kimanin 500 ne za su halarci wurin taron.
Ya ce dukkanin musulmi za su iya mafana da abubuwan da za a tattauna kansu a wajen wannan taro, kai tsaye ne ko kuma ta hanyar bin shiri a yanar gizo ta wannan adireshi productivemuslim.com .
Haka nan kumaya kara da cewa, an afatan wannan ta zama wata hanya ta isar da sako na addini da kuma kyakyawar dangantaka tsakanin musulmi da wadanda ba su ba.