IQNA

Taron Fadakarwa Kan Muslunci A New York

23:22 - April 26, 2016
Lambar Labari: 3480357
Taron Fadakarwa Kan Muslunci A New York
Bangaren kasa da kasa, college Clinton na shirin daukar bakuncin wani taro domin wayar da kai da kuma karawa juna sani dangane da addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Clinton Herald cewa, wannan shiri zai samu halartar malaman majami’oi da kuma wasu daga cikin masana musulmi da kiristoci.

Taron ya hada bangarori daban-daban na addinai da ya hada da su kansu musulmi.

Dr. Anis Ansari wanda shi ne kan gaba wajen gudanar da shirin taron ya bayyana cewa, yana fatan wannan ya zama wata hanya ta samar da fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai.

Ansari ya kara da cewa bababn abin da ya karfafa su wajen gudanar da wannan shiri shi ne, irin halin da musulmi suka samu kansu a ciki a kasashen turai, sakamakon ayyukan ta’addanci da wasu suke gudanarwa da sunan addinin muslunci, wanda hakan yake bata sunan muslunci.

Dr. Ahmadullah Sidghi na daga cikin wadanda za su gabatar da jawabai tare da amsa tambayoyi mahalarta taron, kasantuwarsa daya daga cikin fitattun masana muslmi a kasar.

Lareson wanda malamain kirista ne zai bayani kan addinai masu dangantaka da annabi Ibrahim, yayin da Sidighi zai Magana kana bin ya kamata Amurkaw su sani dangane da muslunci.

A bangare guda kuma za a bayyana wasu daga cikin irin a’adun muslunci da hakan ya hada da saka tufafi da kuma hijabi wanda mata musulmi sukan saka, da wasu daga cikin kayan tarihi.

3491779

captcha