
Kamfanin dillanicin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yam Sabi cewa, a wani faifan bidiyo da aka fitar, an nuna Elgreen dan majalisar dokoki kasar Amurka yan bayyana cewa, musulunci ba addinin ta’addanci ba ne.
Ya ci gaba da cewa, ko shakka babu addinin muslnci ba addinin ta’addanci ba ne kamar yadda wasu suka dauka kuma suke ta yadawa, maimakon hakan ma shi addini ne na zaman lafiya da sulhu da fahimtar juna.
Wannan dan majalisar dokokin Amurka dai ya bayyana wannan furuci ne sakamakon yadda kiyayay da muslunci ke ta karuwa a cikin kasar Amurka, wanda hakan har ya hada da yan siyasa.
Ya bayar da shawar ga masu kiayya da muslunci a kasar da su nemi sanin abin da musulmi suke cewa daga addininsu dagangane da zaman lafiya, kuma su daina yin hukunci da abin da wasu baragurbi daga cikin musulmin suke aikatawa na ta’addanci a matsayin cewa shi ne msuulunci.
A kwanakin baya dai Donald Trump da ke neman takarar shugabanicn kasar ya yi kamalan batunci ga musulmi, tare da bayyana su a matsayin yan ta’adda.