
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran na Anatoli cewa, al’ummar yankin Darfur na kasar Sudan suna amfani da tsarin koyar da karatu Khalwa domin koyar da kur’ani mai girma.
Wanna tsari dai yajima ana gudanar da irinsa a yankin tsawon shekaru,duk kuwa da cewa da dama daga cikin al’ummomin yankin suna fuskantar matsaloli na tsaro tun daga shekara ta 2003.
Hanyar koyar dea kartu ta Khalwa it ace yin amfani da alluna na katako, inda akan rubutua kansu kuma ana karantawa ana nanata tilawa har sai ta zauna, daga nan sai a wanke a kara gaba.
Shi dai wannan salon tsaron karatu na khalwa babu banbaci tsakanin mayan daga kanan yara, domin kuwa tun daga dan shekara biyar har zuwa dan shekara hamsin duk za su iya shiga cikin tsarin.
Abin tuni a nan dais hi ne, kasar Sudan tana daga cikin kasashen da suke bin wannan tsari a mafi yankunan kasar ba sai yankin darfur ba.