IQNA

Matasan Musulmi A Canada Suna Kara Yin Riko Da Addini

17:32 - April 28, 2016
Lambar Labari: 3480362
Bangaren kasa da kasa, wani sakamakon jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a kasar Canada ya nuna cewa da dama daga cikin samari musumi na Canada suna kara yin riko da addini.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CBC NEWs cewa, riko da addini a tsakanin matasan msuulmin kasar Canada ya karu da kimanin kashi 61 cikin dari.

Haka nan kuma sakamakon ya nuna cewa akalla kashi 48 cikin na musulmin suna zuwa masallaci sau guda a mako domin halaratr sallar jam'i.

Haka nan kuma abangaren mata masu saka lullubi a kansu ya karu, ta yadda kimanin kashi 6 daga cikin kuma suna saka hijabi.

Wadanda aka ji ra'ayinsu da dama sun babayyana cewa a cikin shekaru 5 da suka gaba, kyamar msuulmi da cin zarafinsu ya karu matuka a kasar, duk kuwa da cewa musulmi suna kan gaba akowane lokaci kan duk wani batu na zaman lafiya da samar da fahimtar juna a tsakanin al'ummar kasar.

An gudanar da wannan jin ra'ayin jama'a ne dai a tsakanin watan Nuwamban shekara ta 2015 zuwa janairun 2016, kuma kimanin musulmi 600 ne aka ji ra'ayoyinsu.

captcha