
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shfain sadarwa na Anatoli Turkiya AA cewa: a ranar Alhamis da ta gabata ce jami’an tsaron kasar suka kame wani mutum dan asalilin kasar Syria a cikin birnin Islanbul yana hankoron sayar da wani dadadden littafin Attaura wadda ta yi shekaru 600 da rubutawa.
Bisa ga wannan rahoto, wani jami’in yan sanda ne ya yi Magana da wannan mutum ta hanayar yanar gizo a matsayin mai saye, inda suka yi mahada da shi a wani wuri domin gana kuma su kammala ciki, bayan da ya ce zai iya sayen ittafin har zuwa dala miliyan 5 lakadan.
Sun yi mahada a yankin Sultan Ahamd, inda mutumin ya jira mai sayen a wani otel, a nan kuma jami’an tsaro suka cafke shi, inda ya bayyana cewa wannan littafin yana da alaka da danginsa ne a Syria, kma ya shigo da shi Turkiya ne domin ya sayar.
Masu gudanar da gwaji dangane da kayan tarihi sun fara yin gwaje-gwaje akansa, ida suka lallai wannan littafi da gaske ne ya kai wannan shekaru da aka fada.