Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarta cewa a gobe ne idan Allah ya kai mu za a bude babbar karatu da hardar
kur’ani mai tsarki ta duniya a kasar Malayzia tare da halartar sarkin kasar
Abdulhalim Mu’azzam Shah, da kuma baki gami da jami’an diplomasia na kasashen
da aka gayyata.
Babbar cibiyar bunkasa ayyukan muslunci a kasar ta Jakim ta bayyana cewa, kasashe 69 ne za su halarci gasar, wadanda za su halarci bangarori daban-daban na gasar, amma kasashe 26 za su halrci bngarori biyu daga cikin bangarorin gasar kamar dai yadda aka sanar da cibiyar.
Kasamar Malayzia mai masafkin baki tana da masu halartar gasar guda hudu, wadanda suka hada da maza da kuma mata, za su shiga bangaren gasar harda da kuma karatu.
Alkalan gasar dai su 16 da suka fito daga kasashen Masar, saudiyya, Jordan, Qatar, Indonesia, Nurnai, Lebanon, Thailand da kuma Malayzia.
Sayyid Mustafa Hussaini shi ne zai wakilci jamhuriyar muslnci ta Iran a wannan gasa.
A jiya ne ya kama hanya tare da mahaifinsa, da kuma malaminsa Mahammad Abbasi, sai Mahammad Fathi, Muhammad Jabbari wadanda dukkaninsu suna cikin masu gudanar da ayyuka a bangaren kur’ani.