Kamfanin dillancin labaran Iqna ya
habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Alwatan kasar masar cewa, jaridar ta buga
a shafinta taken "Mustafa Hussaini” inda a ciki ta tuna ta makarancin kur’ani
na kasar Iran da ya zo na daya a gasar
da aka gudanar a shekarar da ta gabata.
Alwatan ta rubuta cewa:
Wannan gasa za a gudanar da ita ne tare da halartar kasashen duniya daban-daban a Malayzia tare da halartar kasar Iran, makarancin kur’ani dan kasar Iran matashi Musataf aHussaini shi ne zai wakilci kasar a wannan gasa wadda kasashe 69 ne za su halarci gasar wadanda za su halarci bangarorinta na harda da karatu.
Abin tuni a nan dais hi ne a gasar da aka gudanar a shekarar da ta gabata a karo na 57, Haji Hasani Kargar dan kasar Iran shi ne ya zo na daya, kuma ya yi shahada a kisan gangancin da aka yi kan alahazai a hajjin da ya gabata.
Wadanda za su yi alkalancin gasar dai su 16 da suka fito daga kasashen Masar, saudiyya, Jordan, Qatar, Indonesia, Nurnai, Lebanon, Thailand da kuma Malayzia, kuma ana sa ran sarkin kasar Abdulhalim Mu’azzam Shah ne zai bude taron.