IQNA

An Fara Gasar Kur’ani Ta Duniya A Malayzia

23:08 - May 02, 2016
Lambar Labari: 3480372
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani na duniya a kasar Malayzia a babban dakin taron cibiyar kasuwanci ta birnin Kualalmpour.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an fara gasar ne da misalign karfe 20 daidai na agogon kasar, tare da halartar Jamil Khail Baharam ministan ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar.

Ali Akbar Reza’i shugaban ofishin kula da harkokin al’adu na Iran da manyan jami’ai na tashar talabijin ta Alkauthar da Kur’an Sayyid Jawad Musavi dukkaninsu sun halarci taron bude wannan gasa a birnin Kualalampour.

Sayyid Mustafa Hussaini zai gabatar da karatunsa a ranar Laraba mai zuwa agaban mahalrat wannan gasa.

Wannan gasa ta kasa da kasa, ta kara samun mahalrta daga kasashen duniya, inda kasashen Australia, Holland, Hong Kong, Belgium, Spain, England, Sweden na daga cikin wadanda suke halartar gasar a karon farko.

Mutane 16 za su yi alkalancin gasar da suka fito daga kasashen Masar, saudiyya, Jordan, Qatar, Indonesia, Nurnai, Lebanon, Thailand da kuma Malayzia, wadda ke da masaukin baki.

3494118

captcha