IQNA

Shirin Mayar da Wasu Masallatan Wuraren Hardar Kur’ani

23:21 - May 04, 2016
Lambar Labari: 3480384
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin addini a Masar na shirin mayar da wasu daga cikin masallatan kasar 1000 manyan masallatai na juma’ da kuma hardar kur’ani.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alahram cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini a Masar na shirin mayar da wasu masallatai 1000 daga cikin masallatan kasar masallatai na juma’ da kuma samar da wuraren hardar kur’ania cikinsu.

Muhammad Mukhtar Juma’a minister mai kula da harkokin addini a kasar ta Masar ne ya sanar da hakan, inda yace suna shirin samar da wurare na hardar kur’ani na zamani,amma ta hanayar yin amfani da wasu masallatan kasar, tare da mayar da su masallatai na juma’a.

Yace za a fara aiwatar da shirin ne daga lardin Alkalyubiyya, inda za a fara da masallatai 50 daga cikin wannan lardi wanda yake da yawan masallatai.

Ya ci gaba da cewa wanan shiri ana da zimmar fara aiwatar da shi nea cikin wannan watan azumi mai zuwa, domin al’umma su amfana da shirin kamar yadda ya kamata.

Haka nan kuma yay i ishara da cewa za a gyara wuraren yin taruka na ibada kamar ittikafi da sauransu, kamar yadda kuma za a kebance wrare na karatu da hardar kur’ani mai tsarkia cikin wani bangare na masallaci.

Kamar yadda ya bayyan acewa shi maasallaci ba wuri na salla ba kawai, wuri na yada al’adun a ddini da ilimi da kuma isar da sakon muslunci da koyarwarsa, indsa za a rika fadakar da musulmi dangane da addininsu.

Bisa ga koyarwa ta muslunci dai masallaci yana da sharudda wadanda dole ne e kiyaye su, kuma bayyana wasu masallatan a matsayin wuraren ayyuka na musamman zai bayar da damar kara samun cibiyoyin kara yada koyarwar kur’ani a kasar.

3494787

captcha