Kamfanin dillanicn labaran iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin tashar PressTV cewa, a yyin wannan ganawar
Ali Akbar Wilayati yay i Allawadai da kakkausar murya dangane da saka kungiyar
Hizbullah da wasu larabawa suka yi.
Ya ce ko shakka babu abin da suka yi bababn abin kunya ne, domin bas u taba haduwa suka saka wata kungiyar yan ta’adda a cikin jerin sunayen yan ta’adda ba, bil hasali ma su ne suke daukar nauyinsu, amma a lokaci guda har suna da karfin halin da za su kira Hizbullah kungiyar ta’addanci, wadda da ba domin it aba da sukan su sun zama labara.
Haka nan kuma Wilayati ya gana da wasu daga cikin jami’an kasar Lebanon gami dac wasu daga cikin jagororin kungiyoyin gwagwarmaya mazauana kasar ta Lebanon.
Kamar yadda kuma ya gana da jami’an huldar diplomasiyya na kasar Iran da suke zaune a kasar, inda suka tattauna lamurra da suka shafi yankin.
Shi ma a nasa bangaren Sayyid nasrullah ya bijiro da wasu batutuwa da suka shafi a halin da ake cikin yankin gabas ta tsakiya.