IQNA

Gasar Kur’ani Mai Tsarki A Tsibirin Moris

22:16 - May 06, 2016
Lambar Labari: 3480387
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki a tsibirin Moris da ke kudancin tekun India.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hqmi.org cewa, an gudanar da wannan gasar karkashin shirin Hassan Bin Sabit.

A wannan gasa dai mahardata 29 ne suka halarta, inda aka raba gasar bangarori daban-daban na harda wanda ya hada bangaren maza da kuma bangaren mata.

Haka nan kuma alkalai uku ne suka jagoranci alkalancin gasar, inda aka yaba da yadda ta gudana da kuma irin alkalancin da suka yi a tsakanin masu gudaar da gasar.

An kuma gabatar da jawabai wadanda suke karfafa iyayen yara da su aike da yayansu zuwa makaranta domin koyon karatun kur’ani mai tsarki, da kuma sauran ilmomin addini.

Dagakarshe dai an kamala gasar tare da halartar manyan jami’ai da suka hada da firayi ministan kasar, da kuma wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati, inda aka bayar da kyautuka ga wadanda ska nuna kwazo a wannan gasa.

Tsibirin Moris dai yana gabashin tsibirin Madagaska ne da tazarar kilo mita kusan 900 a cikin tekun India, kuma wannan tsibiri dai ana lissafa shi ne a cikin nahiyar Afirka, wadda ta hada bangarori daban-daban cikin nahiyar da kuma wasu tsibirrai da dama da suke kusa da yankin.

3495312

captcha