IQNA

Sayyid Nasrullah:

Sadiyya Ce Kan Gaba Wajen Yaki Da Gwagwarmaya

21:08 - May 07, 2016
Lambar Labari: 3480389
Bangaren kasa da kasa, bababn sakataren kungiyar Hizbullah a Lebanon ya bayyana gwamnatin Saudiyya da cewa it ace kan gaba a halin yanzu wajen yaki da kungiyar domin kare manufofin Isra’ila a yankin gabas ta tsakiya.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar Alalam cewa, shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar gwamnatin Saudiyya ita ce ummul aba’isin rikicin dake faruwa a yankin Gabas ta tsakiya a kokarin da makiya suke yi na ruguza yankin, yana mai sake jaddada cewar kungiyar Hizbullah tana nan daram da karfinta duk kuwa da makirce-makircen da ake kulla mata.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi wajen bikin da Cibiyar Goyon Bayan Gwagwarmaya ta kungiyar ta shirya a birnin Beirut, babban birnin kasar ta Labanon inda ya bayyana yakin da aka kaddamar kan kasar Siriya a matsayin wani kokari na sahyoniyawa da kawayensu na kawo karshen kungiyoyin gwagwarmaya masu adawa da haramtacciyar kasar Isra’ila a Labanon da kuma Palastinu.

Sayyid Nasrallah ya bayyana cewar: Saboda cimma wannan manufar ce a halin yanzu muke ganin wasu gwamnatoci suna siffatanta kungiyar gwagwarmaya (Hizbullah) a matsayin kungiyar ta’addanci, a tunaninsu hakan zai sanya kungiyar ta rasa irin goyon bayan da take samu.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa wasu gwamnatocin, baya ga kokarin da Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suke yi, suna ta kokari wajen bata sunan kungiyar Hizbullah ta hanyar kiranta da sunan kungiya mai aikata muggan laifuffuka bayan sun siffanta ta da cewa kungiya ce ta ta’addanci, sannan da kuma hukumta duk wanda yake goyon bayanta, don hana duk wani mai shirin taimakonta ya taimaka mata, don kada a sanya masa takunkumi ko kuma a kwace masa dukiyarsa.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Wadannan mutanen suna zaton kungiyar Hizbullah za ta yi rauni ne idan suka haramta mata samun dukiya, wanda hakan zai saukake musu kawo mata hari don ganin bayanta. Sayyid Nasrallah ya ce: A halin yanzu gwamnatin Saudiyya, tare da wadanda suke tare da ita irin su majalisar hadin gwiwan kasashen larabawan Tekun Fasha da kungiyar hadin kan kasashen larabawa, suna kokarin aikata hakan, ta hanyar siffanta kungiyar Hizbullah da cewa kungiya ce ta ‘yanta’adda.

Sayyid Nasrallah ya bayyana cewar: A halin yanzu dai gwamnatin Saudiyya ita ce ja-gaban yakin da aka kaddamar na ruguza yankin Gabas ta tsakiya (da kasashen musulmi), yana mai cewa a halin yanzu dai alaka da kuma tattaunawar da take gudana tsakanin jami’an gwamnatin Saudiyya da jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila ta fito fili, bayan boye-boyen da ake yi a baya da bayyana ta a matsayin wata ganawa ta daidaiku (wacce ba ta da alaka da gwamnatin kasar), kamar yadda ya zargin Saudiyyan da yin kafar ungulu ga duk wani kokari na sulhu da kawo karshen yakin da ke faruwa a kasashen Siriya da Yemen.

A wani bangare na jawabin nasa, Sayyid Hasan Nasrallah ya jinjinawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, musamman Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, saboda irin goyon bayan da suke ba wa kungiyar.

Sayyid Nasrallah ya bayyana Jagora Imam Khamenei a matsayin uba kana kuma mai taimakon kungiyar gwagwarmaya yana mai cewa: Imam Khamenei ya kasance yana tare da mu da goyon bayan mu, da dukiya da karfafa mana ruhi.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Matsayar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci kan taimakon kungiyar Hizbullah, wata matsaya ce wacce ba komai kashin kokwanto cikinta, don haka ne ma a halin yanzu Jamhuriyar Musulunci ta Iran take fuskantar matsin lamba kala-kala da kuma shigo da wasu sabbin batutuwa bayan an rufe batun shirin nukiliyan kasar.

Sayyid Nasrallah dai ya sake jaddada wa masoya da magoya bayan kungiyar ta Hizbullah cewa lalle kungiyar tana nan daram dinta babu wani abin da ya shafe ta ko kuma sanya ta ta yi rauni duk kuwa da makirce-makircen da ake ci gaba da kulla mata.

3495365

captcha