Kamfanin dillancin labaran iqn aya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jawharafm.net cewa, Muhammad Khalil ministan ma’aikatar kula da harkokin addinia
kasar Tunisia ya ce suna da shiri na samar da kwafin kr’anai ga masu
larori na musamman a kasar wanda cibiyar buga littafai ta sarki Fahad a madina
za ta buga.
Ya ce da zaran an kamala aikin za a mika dukkanin kwafin kur’anan da aka buga ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar domin raba su a dukkanin larduna a na kasar, inda hakan zai taimaka matuka ga matune masu fama da larurori na usamman su zama ba a haramta musu amfana daga karatun kur’ani ba.
Daga cikin wadanda shirin zai shafa kuwa har da makafi da kuma krame, wadanda za a buga littafai da yarensu yadda za su iya fahimtar abin da ya kunsa.
Tun kafin wannan lokacin dai mahukunta aTunisia sun saya ya zamawajibi a dukkanin masallatan Juma’a na kasar, da arika gabatar da hudubar Juma’a tare da tarjamata da harshen ishara na kurame.